Sunday, September 16, 2007

MU FAHIMCI SIYASAR MAGABATANMU
Hamisu Musa Isah
Sheka – Barde Kano State, Nigeria.
+2348068979409
hamisumu@gmail.com
muhamisu@yahoo.com

Tun da farkon fari kafin na yi nisa ya kamata na dan waiwaya baya, domin na yi wa ‘yan uwa tuni, akan ma’anar siyasa ta zahiri da kuma badini. Duk da yake mutane sun fi sanin ma’anar siyasa na badini, sanadiyyar irin halin da suka tsinci kansu a ciki. Wannan bay a rasa nasaba da irin mummunar fahimtar da mutanenmu suka yi wa siyasa a wannan lokacin.
Ba tare da yin dogon bayani ba kowa ya san kalmar siyasa aro ta aka yi daga harshen Larabci wato, “ASSIYASAT” amma idan muka dubi ma’anar da Larabawa suka bawa kalmar shi ne: Hanyar mulki ko kuma hanyar sarrafa tunanin mutane domin shugabantarsu. A takaice dai za mu iya cewa siyasa tana nufin hanyar shugabantar al’umma. Wannan shi ne ma’anar siyasa ta zahiri.
Amma idan muka dauki ma’anar siyasa a hausance kokuma n ace ta badini ma’ana ta yadda jama’a suke kallonta a yau. Za mug a cewa takan dauki ma’anar; rashin cika alkawari ko wayo day audara, wasu ma suna yio mata kallon, neman hanyar kodamar handamar dukiyar mutane da cin amana ta hanyar yaudararsu da wasu kyawawan abubuwa da suke burin samu. Shi ne ma a yanzu idan mutum y ace “kar ka yi min siyasa” yana nufin karka yi min wayo ko kar ka yaudare ni. Wannan it ace ma’anar siyasa ta badini.
Bari kuma mu dubi dabiar ‘yan siyasa na da da kuma na yanzu. Ba sai na yi dogon bayani game da magabatanmu a fagen siyasa ba, domin kusan kowa shaida ne a kan irin tubalin siyasar da suka assasa musamman a wannan yanki na arewacin Najeriya, babu shakka sun yi kokari, ba karami ba. Duk da cewa dan adam tara yake bai cika goma ba, ma’ana su ma suna da nasu kurakuran, amma sai dai alkairansu sun fi kurakuran su yawa. Hakan ce ta bas u dammar shahara da kuma samun kwarjini a idanun duniya. Da akwai wani lokaci da Azikwuwe (Zik) ya hadu da Sardauna sai yake cewa da Sardauna “ya kamata mu manta da bambance – bambancen da suke tsakaninmu” amma Sardauna da yake Allah ya yi masahikima da kuma iya zama da jama’a sai ya amsa masa da cewa; “ya kamata dai mufahimci bambance – bambancen da suke tsakaninmu, ni musulmi ne dan arewa, kai kuma kirista ne mazaunin kudancin kasar nan, fahimtar hakan ne zai sa mu samara da dunkulalliyar al’umma(kasa)”
Sai kuma wani abin ban sha’awa ga magabatanmu, shi ne, sub a wai suna yin siyasa ba ne domin arzurta kansu, ko tara wani abin duniya. Mutum zai iya tabbatar da haka, idan ya dubi tarihin wadannan bayin Allah, za ka gad a yawansu sun bar mulki ba su da ko motar hawa da akwai ma wadanda suka bar mulkin ba tare da sun mallaki gida nasu na kansu ba, hasali ma wasu har bashi ake binsu. Kuma hakan bai hana sucimma nasara a rayuwarsu ba. Domin zai yi wuya gari yaw aye rana ta fadi ba ka ji an ambato irin ayyukan alkairin da wadannan bayin allah suka yi ba. Shi yasa ma za ka ga na makala sunayensu a wasu muhimman tituna da kuma gine – ginen gwamnati.
Wani kuma abin ban sha’awa shi ne, wadannan mutane siyasarsu bat a a mutu ko a yi rai ba ce, sukan bar talakawa su zabi wanda suke ganin shi ne ma fi alkairi a gare su. Haka kuma siyasarsu suna yin tan e a bias manufa. Domin kuwa za ka ga kowacce jam’iyya tana da manufofin da ta sa a gaba . wadanda take da niyyar aiwatar das u a lokacin da tai nasarar karbar mulki, kuma samun mulkin ba za sa su canja daga wadannan manufofin ba. Misali jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano, daga cikin manufofinta sun yiwa talakawa alkawarin cewa da zarar sun zabe su, za su soke musu haraji da jangali. Kuma abin day a faru ke nan a lokacin da jam’iyyar PRP ta kafa gwamnati a wancan lokacin a Jihar Kano. Kuma manufofinta na kwatowa talakawa ‘yanci bai canja ba, hakan ne ya sa talakawa suka rike jam’iyyar hannun bi- biyu. Domin sun ga babu alamun yaudara a tattare da jam’iyyar da shugabaninta. To haka ake so kowacce jam’iyya ta kasance.
Haka ma su kansu talakawa a wancan lokacin suna yin siyasa ce ta akida ba wai don su sami abin duniya ba. Domin da yawansu sun yi gudun hijira a sakamakon bambancin ra’ayin siyasa haka kuma da ywa sun yi asarar ayyukansu duk sabuda bambancin ra’ayin siyasa. Haka kuma abin yake idan lokacin zabe ya zo,sukan tsaya ne su ga sun zabi wanda suke ganin ya fi musu alkairi a gare su. Ba wai wanda zai dauko kudi ya ba su ba. Shi ya sa ko da mutum yayi amfani da kudi a wancan lokacin bai cika kai labari ba. Wanann ce ta sa kowa yake ganin mutuncin kowa tsakanin masu zabe da kuma wanda aka zaba. Hatta su ma jami’an zabe sukan yi kokarin su ga sun yi adalci a tsakanin jam’iyyun da suka tsaya takara.
Haka kuma a wancan lokaci jam’iyyun hamayya bas a yanke hulda da jam’iyya mai mulki, musamman idan aka zo hakar gudanar da gwamnati, domin sukan ajiye siyasar a gefe sub a wa gwamnati a kan abin da suka ga zai kawo ci gaban al’umma. Haka ma ita gwamnati ba za ta bijire wa wadannan shawarwarin ba matukar dai tag a suna da amfani kasancewar abokan hamayya ne suka bayar da su. To haka ya kamata ‘yan siyasarmu na yanzu su zama.
Saboda haka nasihata ga ‘yan siyasarmu na wannan zamanin ita ce, ya kamata su ji tsoron Allah a kan duk wani abu da za su yi, domin tsoron Allah shi ne zai yi wa mutum jagoranci ya rika aiwatar da ayyuka na alkairi. Kuma su tuna cewa duk abin da suke yi a nan duniya akwai ranar hisabi, ranar da za a titsiye mutum zai yi bayanin irin ayyukan da ya aikata a nan duniya.
Haka kuma wani abu da ya kamata ‘yan siyasarmu su yi la’akarida shi, shin e magabatanmu ba wai sun yi siyasa ta a mutu ko a yi rai ban e; sukan ba wa kowa damarsa ya zabi wanda ya ga ya kwanta masa a rai, sub a su yin murdiyar zabe. Don haka ya kamata a rinka sakar wa talakawa mara suna zabar wadanda suka ga sun dace das u mulke su.
Nasihata ta gaba ita ce ya kamata ‘yan siyasa su guje wa handama da babakere da kuma wawurar kudin talakawa, wanda ya kamata su yi wa talakawan aiki, domin wannan zalunci mai girma, wanda a karshe mutum zai kare da yin nadama tun ma a nan duniya; za a iya fahimtar haka idan aka kalli yadda takasance a kan wasu tsofaffin gwamnoni wanda wasu daga cikinsu har hawaye suka zubar a gaban kuliya. Kasancewar bas u taba tunanin haka za ta kasance a game da su ba musamman a lokacin da suka shagala da wawurardukiyar talakawansu.
Bahaushe yace idan anbi ta barawo to abita ma bi sawu, domin su kansu talakawa suna da nasu laifin. Domin a kullum ka leka gidan wani maimulkin za ka gan shi a cike fal da ‘yan maula, kuma kowa da irin karyar day a je da ita domin kawai ya biya bukatun kansa. To, ya kamata mu ma talakawa muguje wa wannan mummunar dabi’a.
Allah Ya sa dai mu gane.

No comments: