Sunday, September 16, 2007

MU FAHIMCI SIYASAR MAGABATANMU
Hamisu Musa Isah
Sheka – Barde Kano State, Nigeria.
+2348068979409
hamisumu@gmail.com
muhamisu@yahoo.com

Tun da farkon fari kafin na yi nisa ya kamata na dan waiwaya baya, domin na yi wa ‘yan uwa tuni, akan ma’anar siyasa ta zahiri da kuma badini. Duk da yake mutane sun fi sanin ma’anar siyasa na badini, sanadiyyar irin halin da suka tsinci kansu a ciki. Wannan bay a rasa nasaba da irin mummunar fahimtar da mutanenmu suka yi wa siyasa a wannan lokacin.
Ba tare da yin dogon bayani ba kowa ya san kalmar siyasa aro ta aka yi daga harshen Larabci wato, “ASSIYASAT” amma idan muka dubi ma’anar da Larabawa suka bawa kalmar shi ne: Hanyar mulki ko kuma hanyar sarrafa tunanin mutane domin shugabantarsu. A takaice dai za mu iya cewa siyasa tana nufin hanyar shugabantar al’umma. Wannan shi ne ma’anar siyasa ta zahiri.
Amma idan muka dauki ma’anar siyasa a hausance kokuma n ace ta badini ma’ana ta yadda jama’a suke kallonta a yau. Za mug a cewa takan dauki ma’anar; rashin cika alkawari ko wayo day audara, wasu ma suna yio mata kallon, neman hanyar kodamar handamar dukiyar mutane da cin amana ta hanyar yaudararsu da wasu kyawawan abubuwa da suke burin samu. Shi ne ma a yanzu idan mutum y ace “kar ka yi min siyasa” yana nufin karka yi min wayo ko kar ka yaudare ni. Wannan it ace ma’anar siyasa ta badini.
Bari kuma mu dubi dabiar ‘yan siyasa na da da kuma na yanzu. Ba sai na yi dogon bayani game da magabatanmu a fagen siyasa ba, domin kusan kowa shaida ne a kan irin tubalin siyasar da suka assasa musamman a wannan yanki na arewacin Najeriya, babu shakka sun yi kokari, ba karami ba. Duk da cewa dan adam tara yake bai cika goma ba, ma’ana su ma suna da nasu kurakuran, amma sai dai alkairansu sun fi kurakuran su yawa. Hakan ce ta bas u dammar shahara da kuma samun kwarjini a idanun duniya. Da akwai wani lokaci da Azikwuwe (Zik) ya hadu da Sardauna sai yake cewa da Sardauna “ya kamata mu manta da bambance – bambancen da suke tsakaninmu” amma Sardauna da yake Allah ya yi masahikima da kuma iya zama da jama’a sai ya amsa masa da cewa; “ya kamata dai mufahimci bambance – bambancen da suke tsakaninmu, ni musulmi ne dan arewa, kai kuma kirista ne mazaunin kudancin kasar nan, fahimtar hakan ne zai sa mu samara da dunkulalliyar al’umma(kasa)”
Sai kuma wani abin ban sha’awa ga magabatanmu, shi ne, sub a wai suna yin siyasa ba ne domin arzurta kansu, ko tara wani abin duniya. Mutum zai iya tabbatar da haka, idan ya dubi tarihin wadannan bayin Allah, za ka gad a yawansu sun bar mulki ba su da ko motar hawa da akwai ma wadanda suka bar mulkin ba tare da sun mallaki gida nasu na kansu ba, hasali ma wasu har bashi ake binsu. Kuma hakan bai hana sucimma nasara a rayuwarsu ba. Domin zai yi wuya gari yaw aye rana ta fadi ba ka ji an ambato irin ayyukan alkairin da wadannan bayin allah suka yi ba. Shi yasa ma za ka ga na makala sunayensu a wasu muhimman tituna da kuma gine – ginen gwamnati.
Wani kuma abin ban sha’awa shi ne, wadannan mutane siyasarsu bat a a mutu ko a yi rai ba ce, sukan bar talakawa su zabi wanda suke ganin shi ne ma fi alkairi a gare su. Haka kuma siyasarsu suna yin tan e a bias manufa. Domin kuwa za ka ga kowacce jam’iyya tana da manufofin da ta sa a gaba . wadanda take da niyyar aiwatar das u a lokacin da tai nasarar karbar mulki, kuma samun mulkin ba za sa su canja daga wadannan manufofin ba. Misali jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano, daga cikin manufofinta sun yiwa talakawa alkawarin cewa da zarar sun zabe su, za su soke musu haraji da jangali. Kuma abin day a faru ke nan a lokacin da jam’iyyar PRP ta kafa gwamnati a wancan lokacin a Jihar Kano. Kuma manufofinta na kwatowa talakawa ‘yanci bai canja ba, hakan ne ya sa talakawa suka rike jam’iyyar hannun bi- biyu. Domin sun ga babu alamun yaudara a tattare da jam’iyyar da shugabaninta. To haka ake so kowacce jam’iyya ta kasance.
Haka ma su kansu talakawa a wancan lokacin suna yin siyasa ce ta akida ba wai don su sami abin duniya ba. Domin da yawansu sun yi gudun hijira a sakamakon bambancin ra’ayin siyasa haka kuma da ywa sun yi asarar ayyukansu duk sabuda bambancin ra’ayin siyasa. Haka kuma abin yake idan lokacin zabe ya zo,sukan tsaya ne su ga sun zabi wanda suke ganin ya fi musu alkairi a gare su. Ba wai wanda zai dauko kudi ya ba su ba. Shi ya sa ko da mutum yayi amfani da kudi a wancan lokacin bai cika kai labari ba. Wanann ce ta sa kowa yake ganin mutuncin kowa tsakanin masu zabe da kuma wanda aka zaba. Hatta su ma jami’an zabe sukan yi kokarin su ga sun yi adalci a tsakanin jam’iyyun da suka tsaya takara.
Haka kuma a wancan lokaci jam’iyyun hamayya bas a yanke hulda da jam’iyya mai mulki, musamman idan aka zo hakar gudanar da gwamnati, domin sukan ajiye siyasar a gefe sub a wa gwamnati a kan abin da suka ga zai kawo ci gaban al’umma. Haka ma ita gwamnati ba za ta bijire wa wadannan shawarwarin ba matukar dai tag a suna da amfani kasancewar abokan hamayya ne suka bayar da su. To haka ya kamata ‘yan siyasarmu na yanzu su zama.
Saboda haka nasihata ga ‘yan siyasarmu na wannan zamanin ita ce, ya kamata su ji tsoron Allah a kan duk wani abu da za su yi, domin tsoron Allah shi ne zai yi wa mutum jagoranci ya rika aiwatar da ayyuka na alkairi. Kuma su tuna cewa duk abin da suke yi a nan duniya akwai ranar hisabi, ranar da za a titsiye mutum zai yi bayanin irin ayyukan da ya aikata a nan duniya.
Haka kuma wani abu da ya kamata ‘yan siyasarmu su yi la’akarida shi, shin e magabatanmu ba wai sun yi siyasa ta a mutu ko a yi rai ban e; sukan ba wa kowa damarsa ya zabi wanda ya ga ya kwanta masa a rai, sub a su yin murdiyar zabe. Don haka ya kamata a rinka sakar wa talakawa mara suna zabar wadanda suka ga sun dace das u mulke su.
Nasihata ta gaba ita ce ya kamata ‘yan siyasa su guje wa handama da babakere da kuma wawurar kudin talakawa, wanda ya kamata su yi wa talakawan aiki, domin wannan zalunci mai girma, wanda a karshe mutum zai kare da yin nadama tun ma a nan duniya; za a iya fahimtar haka idan aka kalli yadda takasance a kan wasu tsofaffin gwamnoni wanda wasu daga cikinsu har hawaye suka zubar a gaban kuliya. Kasancewar bas u taba tunanin haka za ta kasance a game da su ba musamman a lokacin da suka shagala da wawurardukiyar talakawansu.
Bahaushe yace idan anbi ta barawo to abita ma bi sawu, domin su kansu talakawa suna da nasu laifin. Domin a kullum ka leka gidan wani maimulkin za ka gan shi a cike fal da ‘yan maula, kuma kowa da irin karyar day a je da ita domin kawai ya biya bukatun kansa. To, ya kamata mu ma talakawa muguje wa wannan mummunar dabi’a.
Allah Ya sa dai mu gane.

Friday, June 15, 2007

BAHAUSHE A SABON KARNI
Duk lokacin da aka yi batun arewacin Najeriya, babu abin da zai fara fadowa mutum a rai sai Malam Bahaushe, domin shi ne ya mamaye wannan yanki mai albarkar noma da mutane da kuma fadin kasa. Kuma tarihi ya tabbatar cewa Bahaushe mutum ne mai karamci da haba – haba da sauran kabilu, musamman makwabtansa. Wannan ce ma ta sa harshen Hausa ya rinka yaduwa a tsakanin wadannan kabilu.
Kasancewa Bahaushe mutum ne mai wayayyen kai, tun daruruwan shekaru da suka shude. Wannan ce ma ta sa ya shahara, ba ma a nahiyar Afirka ba , har ma a duniya baki daya. Wannan daukaka da Bahaushe ya yi ta jawo masa kwarjini a cikin gida da kuma waje. Wanda har ma a wadancan lokuta ake ganin Bahaushe da matukkar daraja, ta inda duk inda ya je ake ba shi kulawa ta musamman kuma yake ba wa sauran kabilu sha’awa.
Wani abin sha’awa Bahaushe bai bata lokaci ba wajen karbar addinin musulunci a matsayin fanninsa na rayuwa. Hakan ya kara masa daukakar da bata misaltuwa, wanda sakamakon haka ne aka haifar da manyan malamai a wannan sashi na arewacin Najeriya.
Idan kuma muka kalli Bahushe ta fuskar siyasa za mu ga cewa, siyasar wancan lokaci ba ta cika ba tare da dan arewa ba. Domin shi ne wanda ya san dabaru da kuma luggar mulki da siyasa. Wannan ce ma tasa har aka samu mashahuran ‘yan siyasa a wannan sashi, wanda suka yi fice ta fuskar kare mutunci da kuma darajar wannan sashi da al’ummarta. Irin wadannan mutane sun hada da; marigayi Malam Sa’adu zungur, Sa Abubakar Tafawa Balewa, Sa Ahmadu Bello Sardauna, da kuma irin su Malam Aminu Kano da dai sauransu.
To, amma idan muka kalli rayuwar Malam Bahaushe a wannan karnin da muke ciki, shin abin haka yake, ko kuma labari ya sha bamban? Hakika labari ya sha bamban, ta fuskar siyasa, addini da kuma rayuwa ta yau-da-kullum. Dan uwa! Za ka yarda da ni idan na ce maka a yau rayuwar Malam Bahaushe tana cikin tsaka mai wuya. Domin a fadin duniya babu kabilar da ta mayar da bara hanyar cin abinci (ma’ana sana’a) sai Malam Bahaushe. Domin za ka ga yara, matasa da magidanta suna yawo kwararo – kwararo, suna bara wai da sunan neman abinci. Alhali kuma akwai kasashe da kabilu da suka fi mu talauci, amma ba za ka same su da irin wannan dabi’a ba. Mu mutuwar zuciya ta hana mu mu nemi na kanmu.
Wani babban abin haushi kuma shi ne yadda ‘yan siyasa suke yin amfani da matasa, a matsayin ‘yan bangar siyasa. Abin takaici ma a nan shi ne yadda wadannan ‘yan siyasa suke saya wa matasa makamai wai domin su taimaka musu wajen tsoratar da abokan hamayya. A wasu lokutan ma har kashe junansu suke yi, wai da sunan yakin neman zabe. Ba ma a nan abin zai ba ka haushi ba sai ka ga yadda wadannan ‘yan siyasa suke daukar nauyin ‘yan daudu da karuwai suke sheke ayarsu, a duk lokacin da aka ce sun fita kanfen. wannan shi kansa abin takaici ne domin yakan haifar da koma baya da kuma rashin ganin wannan al’umma da mutunci.
Hakika marigayi Malam Sa’adu Zungur ya yi gaskiya, a wakarsa ta “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya “ a inda yake cewa:
“Domin fa arewa da hargitsi,
da yawan barna ba kariya.

Matukar arewa da karuwai,
Walla za mu yi kunyar duniya.

Matukar ‘yan iska na gari,
Dan daudu da shi da magajiya.

Da samari masu ruwan kudi,
Ga maroka can a gidan giya”.

Sannan kuma Malam Sa’adu Zungur ya kara da cewa:
“Matukar yaranmu suna bara,
Allah ba ku mu samu abin miya.

A gidan birni da na kauyuka,
Da cikin makarantun tsangaya.

Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu shakka sai mun sha wuya.

Shawarata a nan ita ce: lokaci ya yi da shugabanninmu na arewa za su farka dangane da kalubalen da yake fuskantarmu, ya kamata musamman gwamnatocin Jahohi da na tarayya da ma na kananan hukumomi da ‘yan majalisunmu, kai har ma da ‘yan boko da attajirai, su yunkuro wajen bayar da tallafi da kyautata tarbiyya a tsakanin al’ummar arewacin Najeriya, domin samar da al’umma ta gari.
Sannan kuma wani nauyi da yake wuyan ‘yan siyasa shi ne, ya kamata su rinka la’akari da halin da al’ummarmu take ciki na tabarbarewar al’amura, domin su rinka aiwatar da kyawawan manufofi da kudurori domin ganin an kyautata al’amura a wannan sashi.
Sai kuma wani nauyi da yake kan attajirai da kuma ‘yan boko; su kuma ya kamata su rinka kokarin ba wa matasa tallafi na jari da kuma na karo karatu, domin ganin an yi maganin zaman banza a cikin wannan al’umma.
Su kuwa matasa babban nauyin da yake kansu, shi ne su daina raina kananan sana’o’I, kuma su rinka kokarin dogaro da kuma neman na kansu, domin gujewa zaman kashe wando.
A karshe ina kira ga al’umma baki daya, da mu hada kawunanmu domin ganin mun samar da al’umma ta gari, wadda za mu rinka alfahari da ita a duk inda muka tsinci kanmu. Domin hadin kai shi ne tushen ci gaban al’umma.
Malam Abubakar Ladan Zariya, yana cewa a wakarsa ta “Hadin kan Afirka”
“kwalama hadama ba zai bar mu,
ba mu kai ga mu cimma burinmu,
Son kai haka za girman kanmu,
Shi ke cutar mu da ‘ya’yanmu,
Ba ma kishi na magabatanmu.

Hakika magabatanmu sun yi kokari wajen ganin cewa ba su kawo rarrabuwar kai a cikin al’umma ba. Don haka ya rage namu mu zabi abin yi. Sa’adu Zungur yana cewa:
“mu dai hakkimu gaya muku,
ko ku karba ko ku yidariya.

Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da nadamarmai kin gaskiya.

Friday, May 18, 2007

Hikimata

HARSHEN HAUSA DA KALUBALEN DA YAKE FUSKANTA.
A nan cikin Nijeriya harshen Hausa shi ne na daya a duk kasar, wajen yawan mutanen da suke amfani da shi. za a iya cewa harshen Hausa ya zama tafkin tsakiyar gari idan mutum bai sha ba to wani nasa ya sha. Ana iya cewa kusan ba lungu da sako da ba a magana da harshen Hausa a wannan nahiya.
Harshen Hausa mashahurin harshe ne a duniyar nan tamu,domin shahararsa ta kai ya goga ko ma ya yi kafada - da - kafada da dukkakn manyan harsunan duniya, domin harshe ne da yake da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su da bayyana kowanne irin tunani da su. Shi ya sa ma wani mawaki wato Malam Abubakar Ladan Zariya yake cewa a wakarsa:
"Harshenmu harshe ne a dangin harsuna,
Da muke gadara ko'ina nan duniya,

Har ma yi zaurance da waka ma da shi,
Tamkar su Turanci, Arab baki daya.

Za mu yi rubutu mu yi karatu ma da shi,
Mu alamta littaffai, jaridu bai daya.

Me zai hana ba za mu tashi mu girmama,
Harshe na kakanninmu babu kamar shiya."

Kamar yadda wannan mawaki ya fada, ana iya amfani da harshen Hausa wajen rubuta littattafai da jaridu da mujallu da kuma amfani da shi a kafafen yada labarai na radiyo da talabijin kai har ma da na'ura mai kwakwalwa.
Kodayake yaduwa da bunkasar harshen Hausa ba ya rasa nasaba da irin kwarjini da harshen yake da shi da kuma shaharar da Hausawa suka yi a fagen kasuwanci da fatauci. Hausawa sukan kutsa kowanne lungu da sako na wannan nahiya ta Afirka kai da ma duniya baki daya domin kai haja ko neman aiki ko neman ilmin addini da kuma yada shi. Haka kuma baki sukan yo takakka daga garuruwansu domin kawo haja da kuma saye a kasar Hausa. Wadannan da ma wasu dalilai suka sa harshen Hausa ya bunkasa ya shahara kuma ya gagara a wancan lokacin.
Kwarjini da kuma muhimmancin harshen Hausa a kullum kara bayyanuwa yake yi, kodayake har yanzu babu wata kasar Afirka ta yamma wadda ta mai da wannan harshe ya zama harshen kasa, amma a kan matsayinsa na farko daga cikin manyan harsunan Afirka, mutanen duniya suna daukan cewa babban kuskure ne idan aka banzatar da wannan harshe. Saboda haka manyan kasashen duniya kamar su: Amurka da Rasha da kasar Sin da Ingila da kuma Jamus suka ba wannan harshe babban muhimmanci. Kamar yadda kowa ya sani, wadannan manyan kasashe tuni suka fara yada labarai da harshen Hausa. Bayan haka wadannan kasashe suna kashe kudade da yawa wajen nazari da koyar da wannan harshe. Domin kuwa wani abin alfahari da tunkaho shi ne ba wata jami’a da ta yi shuhura a duniya da ba a koyar da harshen Hausa a cikinta. Wannan ma babban abin alfahari ne ga masu Magana da wanna harshe na Hausa. Kuma wani Karin abin alfahari ga wannan harshe da kuma masu Magana da shi, shi ne a jikin kudin kasarmu Nijeriya babu harshen wata kabila da aka yarda a yi amfani da shi sai harshen Hausa, ma’ana inda aka rubuta adadin kudin da Hausar ajami.
A nan gida Nijeriya haka zalika masana suna bayar da tasu gudummuwar ta fuskar himmatuwa wajen bincike da kuma bunkasa harshen, musamman ta fuskar rubuta littattafai da mukalu da wakoki, muna da irin wadannan mutane dubbai a cikin kasar nan kuma suna yin iya kokarinsu don ganin wannan harshe ya fadada kuma martabarsa ta karu a fadin duniya. Da akwai cibiyoyi da kungiyoyi da hukumomi wadanda suke karkashin wasu jami’o’i da kuma al’ummomin gari da suke ta yin aiki ba dare ba rana don ganin ci gaban wannan harshe.
Duk da irin wannan daukaka da kuma bunkasa da kuma kwarjini da wannan harshe yake da shi , wasu rukuni na mutane da ma daidaiku ba su ma san ana yi ba ‘wai kunu a wani gida’. Domin babban kalubalen da wannan harshen yake fuskanta shi ne, na rashin bin ka’idoji da dokoki da kuma tanade – tanaden wannan harshe. Wannan matsala tana ci wa manazarta da masana da kuma masu kishin wannan harshe tuwo a kwarya, domin matsalar ta zama ruwan dare, a inda za ka ga kafafen yada labarai musamman jaridu, wanda wasu da yawansu ba sa mutuntawa da kuma bin ka’idoji da kuma dokokin rubuta wannan harshe. Wannan babban kalubale ne da wannan harshe yake fuskanta, har ma wasu suna ganin cewa harshen Hausa ba shi da ma wasu tsayayyun ka’idoji da kuma dokoki. Har shi ne ma marigayi Dr. Akilu Aliyu yake cewa, a wakarsa ta “Bahaushe Mai Ban Haushi”

“Kwazo ya kyautu da mu nuna kuzari,
Inganta harshen namu shi ne Hausa.

Ku mu bar kasala sai mu himmatu kun ji,
Zazzage dantse nuna kishin Hausa.”

Haka ma marubuta littattafai, za ka ga wasu ko in ce da yawa daga cikinsu ba sa dora rubutunsu a mizanin wannan harshe, ma’ana ba sa bin dokoki da kuma ka’idojin wannan harshe. Don haka ne ma marigayi Dr. Akilu Aliyu ya kara da cewa:

“wannan abin kunya ina tamka tai,
Harshen wajen kakanka kai ka kasa,

Ya zam abin a yi dariya a yi gwalo,
A gareka don ka fadi ba shan fansa.”

Don haka ya zama wajibi a garemu da kuma duk wani mai sha’awar harshen Hausa, da mu himmatu wajen sani da kuma bin dokoki da kuma ka'idojin rubuta harshen Hausa.
Wata matsalar kuma da take ci wa wannan harshe tuwo a kwarya ita ce ta masu kafa allunan tallace - tallace na manya da kananan kamfanoni da ma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu, a inda za ka ga suna rubuta tallansu da kuma sanarwa da harshen Hausa yadda suka ga dama, ba tare da yin la'akari da dokoki da ka'idojin harshen ba. Wata Hausar ma da ake yin amfani ita a irin wadannan allunan talla , ba ma ta karantuwa.
Hanyoyin magance wadannan matsalaloli su ne:
Ya kamata kafafen yada labarai musamman ma na jarida su danga daukar kwararru, wadanda suka san ka'idoji da kuma dokokin wannan harshe na Hausa, domin kauce wa irin kurakuran da muka ambata a sama.
Bayan haka kuma manyan makarantu da jami'o'inmu musamman sashen koyar da harshen Hausa na wadannan makarantu, su tashi tsaye wajen fadakar da al'umma da kuma ilmantar da su, ta hanyar rubuce -rubuce da kuma bin diddigin irin wadannan kukrakurai domin kawo gyara.
Sannan kuma yana da kyau idan cibiyoyin nazarin Hausa a wadannan jami'o'i su dinga shirya bita akai -akai ga ma'aikatan yada labarai ('yan jarida) da kuma marubuta da masu buga takardu da littattafai domin ganin an kawar da wannan matsala baki daya.
Sai kuma shawara ta karshe, ya kamata su ma kansu malamai da suke koyar da harshen Hausa a makarantun Firamare da Sakandare, su dinga samin damar zuwa karop karatu akai - akai, idan ma haka ba ta samu ba, to, ya kamata a dinga shirya musu bita su ma daga lokaci zuwa lokaci.
Wadannan nan matakai idan aka bi su za a rage irin hawan kawarar da ake yi wa harshen Hausa. A karshe nake rufewa da wakar Malam Sa'adu zungur inda yake cewa:
"mu dai hakkinmu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.

Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da nadamar mai kin gaskiya."