Monday, April 25, 2011

RAYUWAR BAHAUSHE A SABON KARNI

RAYUWAR BAHAUSHE A SABON KARNI
Duk lokacin da aka yi batun arewacin Najeriya, babu abin da zai fara fadowa mutum a rai sai Malam Bahaushe, domin harshen Hausa shi ne ya mamaye wannan yanki mai albarkar noma da mutane wadanda suka shahara ta fannoni daban daban, kama daga fannin ilmi, siyasa da kasuwanci, ga kuma fadin kasa ga Allah Ya ya wadatamu da ita. Kuma tarihi ya tabbatar cewa Bahaushe mutum ne mai karamci da haba – haba da sauran kabilu, musamman makwabtansa. Wannan ce ma ta sa harshen Hausa ya ya shahara ya rinka yaduwa a tsakanin wadannan kabilu.
Bahaushe mutum ne mai wayayyen kai, tun daruruwan shekaru da suka shude. Wannan ce ma ta sa ya yi fice ta fannoni da dama, ba ma a nahiyar Afirka ba , har ma a duniya baki daya. Wannan daukaka da Bahaushe ya yi ta jawo masa kwarjini a cikin gida da kuma waje. Wanda har ma a wadancan lokuta ake ganin Bahaushe da matukkar daraja, ta inda duk inda ya je ake ba shi kulawa ta musamman kuma yake ba wa sauran kabilu sha’awa.
Wani abin sha’awa Bahaushe bai bata lokaci ba wajen karbar addinin musulunci a matsayin fanninsa na rayuwa. Hakan ya kara masa daukakar da bata misaltuwa, wanda sakamakon haka ne aka haifar da shahararrun malamai da masana a wannan sashi na arewacin Najeriya.
Idan kuma muka kalli Bahushe ta fuskar siyasa za mu ga cewa, siyasar wancan lokaci ba ta cika ba tare da dan arewa ba. Domin shi ne wanda ya san dabaru da kuma luggar mulki da siyasa. Wannan ce ma tasa har aka samu mashahuran ‘yan siyasa a wannan sashi, wanda suka yi fice ta fuskar kare mutunci da kuma darajar wannan sashi da al’ummarta da kuma hadin kan kasa baki daya. Irin wadannan mutane sun hada da; marigayi Malam Sa’adu zungur, Sa Abubakar Tafawa Balewa, Sa Ahmadu Bello Sardauna, da kuma irin su Malam Aminu Kano da dai sauransu.
domin al’umma shaida ne a kan irin tubalin siyasar da wadannan shahararrun ‘yan kishin kasa suka assasa musamman a wannan yanki na arewacin Najeriya, babu shakka sun yi kokari, ba karami ba. Hakan ce ta ba su damar shahara da kuma samun kwarjini a idanun duniya. Da akwai wani lokaci da Azikwuwe (Zik) ya hadu da Sardaunan Sokoto sai yake cewa da Sardauna “ya kamata mu manta da bambance – bambancen da suke tsakaninmu” amma Sardauna da yake Allah Ya yi masa hikimar iya magana da kuma zama da jama’a sai ya amsa masa da cewa; “ya kamata dai mufahimci bambance – bambancen da suke tsakaninmu, ni musulmi ne dan arewa, kai kuma kirista ne mazaunin kudancin kasar nan, fahimtar hakan ne zai sa mu samara da dunkulalliyar al’umma(kasa) mai dorewa”
To, amma idan muka kalli rayuwar Malam Bahaushe a wannan karnin da muke ciki, shin abin haka yake, ko kuma labari ya sha bamban? Matukar za mu yi wa kanmu hukunci na adalci za mu tabbatar cewa hakika labari ya sha bamban, ta fuskar siyasa, addini da kuma rayuwa ta yau-da-kullum. Dan uwa! Za ka yarda da ni idan na ce maka a yau rayuwar Malam Bahaushe tana cikin tsaka mai wuya. Domin a fadin duniya babu kabilar da ta mayar da bara hanyar cin abinci (ma’ana sana’a) sai Malam Bahaushe. Domin za ka ga yara, matasa da magidanta majiya karfi suna yawo kwararo – kwararo da garuruwa har ma da kasashen ketare, suna bara wai da sunan neman abinci. Alhali kuma akwai kasashe da kabilu da suka fi mu talauci, amma ba za ka same su da irin wannan dabi’a ba. Mu mutuwar zuciya ta hana mu mu nemi na kanmu.
Wani babban abin haushi kuma shi ne yadda ‘yan siyasa suke yin amfani da matasa, a matsayin ‘yan bangar siyasa. Abin takaici ma a nan shi ne yadda wadannan ‘yan siyasa suke saya wa matasa makamai da kwayoyi da sauran abubuwan sa maye wai domin su taimaka musu wajen tsoratar da abokan hamayya. A wasu lokutan ma har kashe junansu suke yi, wai da sunan yakin neman zabe. Ba ma a nan abin zai ba ka haushi ba sai ka ga yadda wadannan ‘yan siyasa suke daukar nauyin ‘yan daudu da karuwai suke sheke ayarsu, a duk lokacin da aka ce sun fita kanfen. wannan shi kansa abin takaici ne domin yakan haifar da koma baya da kuma rashin ganin wannan al’umma da mutunci.
Hakika marigayi Malam Sa’adu Zungur ya yi gaskiya, a wakarsa ta “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya “ a inda yake cewa:
“Domin fa arewa da hargitsi,
da yawan barna ba kariya.

Matukar arewa da karuwai,
Walla za mu yi kunyar duniya.

Matukar ‘yan iska na gari,
Dan daudu da shi da magajiya.

Da samari masu ruwan kudi,
Ga maroka can a gidan giya”.

Sannan kuma Malam Sa’adu Zungur ya kara da cewa:
“Matukar yaranmu suna bara,
Allah ba ku mu samu abin miya.

A gidan birni da na kauyuka,
Da cikin makarantun tsangaya.

Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu shakka sai mun sha wuya.

Shawarata a nan ita ce: lokaci ya yi da shugabanninmu na arewa za su farka dangane da kalubalen da yake fuskantarmu, ya kamata musamman gwamnatocin Jahohi da na tarayya da ma na kananan hukumomi da ‘yan majalisunmu, kai har ma da ‘yan boko da attajirai da malaman addini, su yunkuro wajen bayar da tallafi da kyautata tarbiyya a tsakanin al’ummar arewacin Najeriya, domin samar da al’umma ta gari.
Sannan kuma wani nauyi da yake wuyan ‘yan siyasa shi ne, ya kamata su rinka la’akari da halin da al’ummarmu take ciki na tabarbarewar al’amura, domin su rinka aiwatar da kyawawan manufofi da kudurori domin ganin an kyautata al’amura a wannan sashi.
Sai kuma wani nauyi da yake kan attajirai da kuma ‘yan boko; su kuma ya kamata su rinka kokarin ba wa matasa tallafi na jari da kuma na karo karatu, domin ganin an yi maganin zaman banza da shaye – shayen miyagun kwayoyi a cikin wannan al’umma.
Su kuwa matasa babban nauyin da yake kansu, shi ne su daina raina kananan sana’o’I, kuma su rinka kokarin dogaro da kuma neman na kansu, domin gujewa tozarta da zaman kashe wando.
A karshe ina kira ga al’umma baki daya, da mu hada kawunanmu domin ganin mun samar da al’umma ta gari, wadda za mu rinka alfahari da ita a duk inda muka tsinci kanmu. Domin hadin kai shi ne tushen ci gaban al’umma.
Malam Abubakar Ladan Zariya, yana cewa a wakarsa ta “Hadin kan Afirka”
“kwalama hadama ba zai bar mu,
ba mu kai ga mu cimma burinmu,
Son kai haka za girman kanmu,
Shi ke cutar mu da ‘ya’yanmu,
Ba ma kishi na magabatanmu.

Hakika magabatanmu sun yi kokari wajen ganin cewa ba su kawo rarrabuwar kai a cikin al’umma ba. Don haka ya rage namu mu zabi abin yi. Sa’adu Zungur yana cewa:
“mu dai hakkimu gaya muku,
ko ku karba ko ku yi dariya.

Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da nadamarmai kin gaskiya.

Daga: Hamisu Musa Isah,

Shekar – Barde,

Kano state.

08068979409.

hamisu_isah­@yahoo.com

http:\\bahaushensabonkarni.blogspot.com