Sunday, January 11, 2009



AL’ADUNMU MUTUNCINMU: KOWA YA BAR GIDA, GIDA YA BAR SHI

Hamisu Musa Isah,

Shekar - Barde, Layin Gidan Maikantu,

Kumbotso L.G. Kano State

08068979409/08027996814

hamisu_isah@yahoo.com

Kalmar al’ada asalinta daga kalmar Larabci take. Kasancewar Bahaushe a ma fi yawan lokaci hankaka ne maiyar da dan wani naka. Sai ya ari kalmar yake yin amfani da ita. Kalmar al;ada dai a Hausance tana nufin hanyar gudanar da rayuwar al’umma. Musamman hanyoyin rayuwa na yau da kullum wadanda al’umma ta saba da su.

Kuma kowacce al’umma tana da nata al’adun wadanda take tunkaho da su. Muhimmin abin da ya kamata mu sani, kafin bayani ya yi nisa, shi ne, al’ada gida biyu ta rabu. Wani zai yi mamaki ya ji an ce al’adu sun rabu gida biyu. To, ba abin mamaki ba ne. Ta farko ita ce al’adun gargajiya, wadanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni, kamar irinsu tufafi da tsarin sarauta da sauransu.

Game da kashi na biyu kuwa su ne, al’adu na aro, ma’ana bakin al’adu. Wadannan bakin al’adu su ne irin wadanda al’ummar Hausawa suka aro daga wasu al’ummomi, musamman wadanda suka yi ko suke yin cudanya da su. Wadannan al’ummomi za su iya zama makwabtansu na kusa da kuma na nesa.

Kafin na yi nisa bari na dan koma baya kadan. A nan zan dan yi wani tambihi ne game da al’adun Bahaushe na gargajiya. Domin mutane su fahimta cewa, akwai kyakkyawa, akwai kuma maras kyau. Kasancewar Bahaushe ya karbi addinin musulunci. Kuma ka’ida ce ta addinin musulunci yakan yi wa al’adun al’ummomin da ya samu abubuwa guda uku.

Na farko dai, idan wadannan al’adu sun dace da dokoki da kuma koyarwar addinin to yakan karba tare da bayar da kwarin gwiwar aiwatar da su. Abu na biyu kuma da addinin yake yi wa al’adu shi ne, yi musu kwaskwarima ko gyare – gyare domin su dace da dokoki da kuma koyarwar addinin. Abu na uku kuwa shi ne, addini yakan yi fatali tare da watsi da al’adu wadanda suka yi hannun riga da wannan addinin.

Kamar yadda muka fada a sama al’ada na nufin, hanyar gudanar da rayuwar al’umma. Wannan ce ma ta sa idan mutum yana son ya gane ko kuma ya fahimci al’adun wata al’umma, mataki na farko da zai bi shi ne, ya yi nazarin hanyoyin rayuwar wannan al’umma. Wannan ce za ta ba shi damar gane al’adun wannan al’umma.

Kamar kowacce al’umma, ita ma al’ummar Hausawa tana da nata al’adun wadanda suke yi mata jagoranci a hanyar gudanar da rayuwar al’ummarta. Sai dai ba a nan gizo yake saka ba. Wadannan al’adu sun gamu ko suna gamuwa da cikas ko kuma koma baya, musamman a halin da muke ciki a yanzu. Duk da cewar Bahaushe yana da himma da kuma kokarin kare martabar al’adunsa. To, amma mene ne yake jawo irin wannan koma bayan da ake samu, musamman ma a wannan lokacin da muke ciki? Akwai dalilai da yawa wadanda za a iya ta’allakasu da wannan halin da muke ciki. Daga cikin wadannan dalilai akwai na nesa da kuma na kusa. Daga cikin na nesa; za mu iya cewa dalilin ya samo asali ne tun lokacin da Turawan mulki mallaka suka shigo wannan yanki namu mai albarka na arewacin Nijeriya. Ma’ana lokacin da suka yi mana cin mutunci na farko, wato lokacin da suka samu nasarar far wa rundunar Sarkin musulmi Attahiru suka yi musu kisan kare dangi. Bayan sun yi musu haka ne suka dawo suka tambayi tsirarun sarakuna da suka rage, cewa ko da wanda yake son yin shahada irin ta Sarkin Musulmi Attahiru? A lokacin wasu daga sarakunan suka bi dare suka sulale, wasu tsiraru kuma suka mika wuya. To, in gajarce muku labari tun daga wannan mika wuya ne aka fara samun canji a al’adun Hausawa musamman ta fuskar mulki. Idan mai karatu bai fahimta ba bari na yi masa dalla – dalla ko zai fahimci abin da nake nufi na canjin da aka samu.

Wato dai daga wancan lokacin sai nadin sarki ya bar hannun Daular Usmaniyya dake Sokoto, domin kafin zuwan Turawa, Daular Usman dan Fodiyo ce take da iko da kuma alhakin nada sarki da ke karkashin wannan Daular. To amma zuwan Turawa sai suka ce daga wancan lokaci wannan ta kau. Ma’ana kowanne sarki cin gashin kansa yake yi. Turawa suka yi amfani da wannan dama da suka samu ne domin su rarraba kawunan sarakunan Daular Usmaniyya. Wato idan muka yi la’akari kuma muka yi nazarin wannan mataki za mu ga cewa al’adunmu na kwarai da suka fara raunana, su ne na zumunci da girmamawa da ke tsakanin wannan daula mai albarka ta Usmaniyya. Hakika wannan rauni da suka yi mana idan ba wani iko na ubangiji ba, har mu koma ga mahaliccinmu ba za mu iya magance shi ba. Hasali ma abin kullum dada lalacewa yake yi. Turawa sun yi mana haka ne, domin sun riga sun san inda baki ya karkata nan yawu ke zuba. Ma’ana sun fahimci cewa talakawa suna yin biyayya ne da kuma koyi ga magabata musamman sarakuna, don haka ne ma suka fara ta kan sarakunan. Da suka fahimci wasu daga cikin sarakunan sun mika wuya. Sai suka fito da wata sabuwar manakisar. Wato tsarin nan na mulki ta bayan fage “Indirect Rule” wanda shi kansa ya taka muhimmiyar rawa wajen gurbatawa da kuma nakasta kyawawan al’adun al’ummar Hausawa misali, tun da Turawa suka gabatar da wannan tsari ne sai sarakunanmu suka bar karbar oda daga daular Usmaniyya, sai dai daga wurin sarauniyar Ingila ta hannun Turawan mulkin Mallaka. Na tabbatar ba za ku bi ni bashin rantsuwa ba, idan na ce maku wannan ce ta jawo talakawa suka fara yanke kauna ga shugabanninsu (sarakuna) na wancan lokacin, domin a da suna ganin babu ya su amma yanzu sai ga shi ba su da ikon ma su zauna a fada sai da yardar Turawa. Don haka wannan ta sa talakawa suka fara saka wa wasu daga cikin sarakunan wancan lokacin ayar tambaya, suna tunanin shin kuwa wadannan su ne shugabanninmu da muka sani ko dai wasu ne daban. Marigayi Malam Sa’adu Zungur a wakarsa ta ‘Arewa Jumhuriya ko Mulukiya’ yana cewa:

“Don akwai wasu ma a sarakuna,

Mun bar su da ayar tambaya.

Hakkin jama’a na kansu duk,

Surike igiyarsa da gaskiya.

Don haka irin wadannan tambayoyi sai suka rinka saka tantama da kuma yanke kauna a zukatan talakawa ga shugabanninsu. Daga nan kuma sai Turawa suka fara bijiro da wasu matakan yaudarar suna nunawa talakawa cewa, su ne kawai za su iya fitar da su daga wannan kangi da suke ciki. Wanda dama haka suka shirya (Turawan). Domin dama sun zo ne don su farraka tsakanin talakawa da kuma shugabanni (sarakuna) na asali, cikin hikima da kuma yaudara. Saboda su samu su shiga tsakani. Bahaushe ma yana cewa: “sai bango ya tsage kadangare yake samun wurin buya”. Don haka suka rasa wurin fakewa sai suka yi amfani da karfi da kuma yaudara suka tsaga bangon suka shiga. Bayan ma sun shiga sai suka fara yin kokarin rushe katangar domin kada a sami wani maginin ya yi tunanin gyara wurin da suka tsaga. Marigayi mai alfarma sarkin musulmi Attahiru kafin ya yi shahada ya rubuta waka da ya saka mata ‘Wakar Zuwan Annasara’ a inda a ciki yake cewa:

“Idan iko kakai kak ko ki tashi,

Ina iko yakai ikon Nasara.

Idan sun baka kyauta kada ka amsa,

Dafi na sunka ba ka guba Nasara.

Suna foro garemu mu bar zalama,

Mazalumta da kansu diyan Nasara.

Bakar fitina gare su da kau makida,

Ta bata dinin musulmi Annasara.”

Saboda haka mataki na farko da suka dauka na kawar da sarakuna daga fagen mulki shi ne, mataki ko kuma na ce shawarar da suka yanke a shekarar 1914, wato shekarar da suka yi wa wannan kasar auren dole. Watakila mai karatu zai yi mamaki ya ji an ce an yi wa wannan kasar auren dole. To ba wani abu ake nufi da auren dole ba, sai lokacin da Turawa suka hade sassan kasar nan wuri guda, wato suka hade kudanci da kuma arewacin kasar nan, karkashin walliccin wani hatsabibin Bature wai shi Lugga “Lugard”

Hakika wannan aure ya jawo matsaloli musamman ma mu a nan arewacin Nijeriya ta fuskar kyawawan al’adunmu. Domin an je an dauko mana wasu mutane da ba mu da wata alaka da su daidai da ta cin abinci, an ce wai ‘yan uwanmu ne. Ba ma a nan abin ya tsaya ba, wai har nuna mana ake yi wai duk daya muke da su bayan kowa ya riga ya san akwai bambance – bambance mai tarin yawa a tsakaninmu. Wannan ya yi matukar kawo mana koma baya ta fuskar gudanar da mulki da kuma aiwatar da rayuwarmu ta yau da kullum. Malam Mudi Sipikin yana cewa a wakarsa ta “Itaciyar Zumunta”

“Me za mu ce da zamanin nan namu,

Domin cikinsa a yanzu babu zumunta.

Ko yalla ya jama’a kuna lura kuwa,

Yau ga shi duk al’adarmu an juya ta.

Manyan abubba masu kyau da muke da su,

Tun zamanin DA yanzu an lalata.

Tun zamanin da NASARA sadda ya bayyana,

Sha’aninmu al’adunmu an rushe ta.

Kuma ga abubba wanda ba su da kyan gani,

Sun afku sun wuce ma adai lasafta.

Kuma wata wauta da Turawan suke yi ita ce; wai sai su rinka cewa mu mance da wadannan bambance – bambancen da suke tsakaninmu(maimakon mu fahimci bambance – bambancen da suke tsakaninmu) mu zamanto kasa daya al’umma daya kuma wai makoma daya. Hakan ba laifi ba ne, to amma abin da ya fara fado min a rai shi ne, ta yaya mutum zai manta da asalinsa da addininsa da kuma kyawawan al’adunsa na gargajiya da ya gada tun iyayen da kakanni. Domin wannan kira da suke yi na munce da bambancin da yake tsakaninmu; suna yin kira ne da mu manta da asalinmu da al’adunmu da kuma addininmu saboda su sami damar cusa mana nasu gurbatattun dabi’un da al’adun. Allah ya saka wa hamshakin dan siyasa alokacin magabatanmu da alheri, musamman a inda yake cewa: “ Nijeriya kasa daya ce amma kowa ya san gidan ubansa” wannan batu haka yake domin kuwa kowa kansa ya sani da kuma al’ummarsa. Bai kamata na wuce wannan turbar ban kawo misalin wata hira da wasu manyan ‘yan siyasarmu na dauri suka taba yi ba, wato tsakanin Gamji Sa Ahmadu Bello Sardauna da kuma Azikuwie (Zik), yadda hirar tasu ta kasance kuwa shi ne, a lokacin da Zik ya hadu da Sardauna sai yake cewa: “ya kamata mu manta da bambance – bambancen da suke tsakaninmu”. A nan ne fa sai Sardauna ya ba shi amsa kamar haka: “A’a ya kamata dai mu fahimci bambance –bambancen da ke tsakaninmu. Ni dan arewa ne kuma musulmi, haka kuma kai (Zik) dan kudancin kasar nan ne kuma mabiyin addinin Almasihu. Ta fahimtar wadannan bambance – bambance ne za mu iya samar da hadin kai a wannan kasa tamu ( Nijeriya)”. Irin wannan matsayi da su Sardauna suka dauka ya dada jawo musu kwarjini a idanun duniya, ba ma wai nan kasa Nijeriya ba, har ma ake yi musu kallon tamkar iyaye ne a siyasar Afirka. Abin tambaya a nan shi ne wai shin su Sardauna barin asalinsu ne ya sa suka shahara ko kuwa riko da kyawawan dabi’u ne da kuma koyi da magabata ya sa suka shahara? Amsar wannan tambaya a bayyane take, saboda magabatanmu sun hango irin illar da take a tattare da tsarin mulkin da Turawan mulkin mallaka suka gabatar mana a wancan lokacin, don haka ne ma suka ki yarda su saki jiki da wannan tsarin domin fahimtarsu ya yi hannun riga da kyakkyawan tsarin da muka gada tun kaka da kakanni. Saboda haka ne ma suka rinka yin kokarin gargajiyantar da irin wadannan tsare-tsare da kuma fahimtar da al’umma da kuma wayar musu da kai game da dukkan wani tsari da aka gabatar musu da shi, wanda ya sabawa al’ada da kuma addini.

Abin da nake so a fahimta a nan shi ne ba wai kowanne tarko ne da Turawa suka dana mana muka fada ba. Domin mun yi nasarar tsallake wasu daga cikin wadannan tarakuna; kamar yadda wasu daga cikin tarkunan nasu (Turawa) suka kama mu a wuya.

Haka dai Turawa suka ci gaba da zabarin al’adunmu na kwarai da kuma addininmu domin ganin sun cusa mana sababbi marasa inganci. Gabatar da ilmin boko ya yi matukar tasiri ga rayuwar al’ummar kasar Hausa; kasancewar tun farko muna da tsarin ilmin addinin da kuma nakaltar yadda za a rubuta a kuma karanta haruffan Larabci. Kodayake makarantun farko da aka fara kafawa a garuruwan Lokoja da Wusasa ta Zariya na ‘yan Mishan ne. Shi kansa wannan dalili ya jawo gagarumin tarnaki ga karbuwa da kuma fahimtar ilmin boko. To amma daga baya gwamnatin Turawan mulkin mallaka ta kakkafa nata makarantun wadanda kafin a kafa su an yi wata kididdiga ta makarantun allo wanda su Turawan suka gano muna da makarantun addini sama da dubu ashirin da biyar a sakamakon binciken da Turawan suka yi da kansu. Ganin haka ne ya sa Turawa suka tabbatar zai yi musu wuya su gabatar da makarantun boko kai tsaye. Don haka sai suka fara da koyar da karatu da rubutu da kuma lissafi shi ne a Turanci suke ce masa “Tripple R ( Reading , Writing & Arithemetics)”. Kasancewar a Arewacin Kasar nan addinin musulunci shi ne kan gaba a cikin zukatan al’ummar wannan yanki sai suka rinka hadawa da koyar da Larabci; amma sai koyar da Larabcin ya zama kamar sinadarine, domin dama an tsarma shi ne domin a jawo hankalin al’umma su karbi karatun boko. Ba wai ina son na nuna cewa karatun boko ba shi da muhimmanci ba ne ba, a’a abin da nake so a fahimta a nan shi ne; su Turawa sun gabatar mana da karatun boko ne tun a wancan lokacin domin kawai su sami saukin gudanar da harkokin mulki. Saboda kudin da suke kashewa a wancan lokacin na harkokin gudanarwa ya yi yawa kasancewarkasar ta yi masu girma. Don haka ya zamar musu dole su jawo ‘an kasa domin taya su harkokin gudanar da mulki, don haka idan mun lura za mu fahimta cewa tun farko ba wai sun gabatar da karatun boko ba ne domi ilmantar da al’ummar Najeriya ba, sai domin biyan bukatar kansu. Daga baya ne kuma da tafiya ta yi nisa suka rinka shigar da wasu darussan har abin dai ya kawo yanzu.

Duk da cewa Turawasun san musulunci shi ne addinin da ya mamaye arewacin nijeriya, to amma ba su yi la’akari da haka ba a lokacin da suka fara gabatar da karatun boko a arewacin Nijeriya duk da cewa sun tsarma harshen Larabci da na Hausa a cikin manhajar karatun; to amma ba a ba shi muhimmanci ba a kan sauran darussa na boko ba. Haka kuma a tsara tafiyar karatun ba su yi la’akari da cewa Asabar da Lahadi ba su ne ranakun hutu a arewacin Nijeriya ba. Mu a wancan lokacin Alhamis da Juma’a muka sani ranakun hutu. Kuma kasancewar su ne ranakun hutu, mafi akasarin al’ummar kasar Hausa sun fi amfani da ranar juma’a domin kai wa ‘yan uwansu ziyara. Musamman yara, ana tura su gidajen ‘yan uwansu domin su kai ziyarar sada zumunci sannan su gaishe su. To amma kasancewar karatun bokko ya gifta ta Alhamis da Juma’a sai aka fara samun rauni ta bangaren zumunci da kuma ziyartar ‘yan uwa, wanda abin kullum dada lalacewa yake an gagara a gyara. Hangen haka ne ma ya sa marigayi Mallam Sa’adu Zungur yake cewa a cikin shahararriyar wakarnan tasa ta “Arewa Jumhuriyya ko Mulukiya”

“A arewa zumunta ta mutu,

sai nashadi sai sharholiya.

Shi kuma Mallam Mudi Sipikin cewa yake yi:

“Jama’a ku gane kar fa tarin dukiya,

ko don talauci har ku manta zumunta.

Ni dai nasiha ce nake nuna muku,

In kun bi lalle za ku san hairinta.

Don Allah kar Ibilis ya dinga batar da ku,

Ban zabe kaina har ku ce na manta.

Wani kokarinmu na son kasa ta yi arziki,

Wallahi sai mun lura mun daidaita.

Mu kula da hakkin ‘yan uwa mu yi taimako,

Ko masu hanya ne bare matalauta.

Mu kula ziyarar ‘yan uwa bisa ko washe,

Kullum mu zam lura muna gyarata.

Wallahi in dai mun kula har mun rike,

Dukkan jidali Rabbi zai maganta.

Akwai wata illa da Turawa suka yi mana wadda mtane da yawa ba su fahimce ta ba. Wannan ba wata illa bace illa raba shugabanni da talakawa; ma’anan idan mai karatu ya lura zai ga lokacin da Turawan mulkin mallaka suna jagorantar wannan kasa duk gidajensu a wajen gari suka je suka gina su, haka kuma ma’aikatu da kuma ofisoshingwamnati duk sai aka tsame su daga cikin al’umma (talakawa). Sabanin yadda muka saba a gargajiyance inda za ka ga gidan sarki a tsakiyar gari kuma koyaushe a cikin ganawa da talakawansa yake. To amma gogayen naka (Turawa) sai suka canja al’amarin. Kuma har yanzu haka al’amarin yake duk inda za ka ga gidan gwamnati ko sakatariyar karamar hukuma, to za ka gansua can gefen gari kewaye da jami’an tsaro kamar wani gidan kurkuku.

Wannan ce ta sa talakawa suke da shakku a kan shuwagabanninsu ta inda za a rinka samun misayar zafafan kalamai tsakanin shugabanni da kuma talakawan da ake mulka. Wanda a karshe za ka ga talakawa suna jifan shugabanninsu wanda yin hakan bakon al’amari nea cikin al’adunmu na gargajiya da ma addininmu.

Wani zagon kasa kuma da Turawa suka yi mana ta fuskar addini ita ta fannin aiwatar da shari’a. Lokacin da Turawa suka zo sun same mu da tsarin shari’a na musulunci wanda ta samo asali daga Alkur’ani da Hadisan Annabi. To, amma da zuwan Turawasai suka ce wai akwai gyara a tsarin tafiyarda shari’ar islama da muke yi, ganin cewa zai yi musu matukar wahala su kawar da tsarin shari’ar musulunci kai tsaye, sai suka kasa laifuka da kuma kotuna zuwa nau’ika biyu, ma’ana laifi ko shari’ar da suka shafi manyan laifuka, sai kai su kotunan da Turawan suke jagoranta. Amma shari’un da suka shafi rabon gado da rikicin aure da makamantansu sai aka bar su a kutunan da suke kiran su da sunan kotunan gargajiya, wanda suke yanke hukunci ta yin la’akari da abinda suka kitra da kundin dokokin shari’a (Penal Code).don haka aka jingine Kur’ani da Hadisi aka maye gurbinsu da tsarin “Penal Code” domin yanke hukunci.

Wannan irin katsalandan da Turawa suka yi mana ta fuskar shari’a ya yi matukarmayar da hannun agogo baya. Kasancewar irin jahadi da kuma dauki ba dadi da Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo ya yi don ganin ya tabbatar da tsarin shari’a da kuma daular musulunci a arewacin Nijeriya. Kuma ya ci nasara alokacinda gabadayan arewacin Nijeriaya da makwabtansu suka zama karkashin daular Usmaniyya. Wannan ce ta sa shari’ar musulunci ta kafu da digadiganta. Amma zuwan zuwan Turawan mulkin mallaka sai da suka targada ta, ma’ana suka yi mata kafa daya ta hanyar shigo da bakin abubuwa ta bayan gida.

Kamar yadda masan suka zayyana tufafin Hausawa suna daya daga cikin tufafin da ake tunkaho da su musamman ma yaddasuke da nau’o’I da dama kamar su: Binjima da kaftani da jauha da bulla da aska takwas ga kuma irin su barage da dasauran riguna wadanda Hausawa ke sakawa wanda idan muka ce za mu lissafto su lokaci ba zai bar mu ba. Kuma wani abin ban sha’awa shi ne, kowanne jinsi da kuma rukuni na mutane yana da nasa nau’in na tufafi. Misali, tufafin mata daban take da na maza. Haka kumatufafin saraki yasha bamban da na talakawa, sannan kuma tufafin malamai ya sha da na attajirai. Haka kuma na dattawa sun shabamban da na matasa. Wannan ce ma tasada kaga Bahaushe a zamanin da kai tsaye za ka gane irinmatsayinsa dakuma rukunin da ya fito a cikin al’umma.

Duk da baiwar daAllah ya yi mana ta wadatattun tufafi masu kima da alfarma, mun yi watsi da su a yau, wato mun yi abin nan da muke cewa ‘sakin na hannu kamun na guje’ ko kuma na ce ‘Jifan gafiyar Baidu’. Ma’ana mu muna yin kokarin watsi da namu tufafin, muna aro na wasu , wadanda ba su dace da al’adunmu ba. Irin wannan dabi’a tamu ce ta sa mashahurin marubucin wakokin Hausar nan Mallam Abubakar Ladan Zariya yake nusar da mu a wata waka da ya rubuta yake cewa:

“Jama’a mu bar sha’awar ado marar kwarjini,

wanda babu tushe, babu asali ko daya.

Mu yo adon suturunmu wanda muke da su,

Duka mai tsiraici yai ji kunyar duniya”.

Abin lura a nan shi ne, irin tufafin da muke yin amfani da su a yau, sun sabawa tarbiyya da kuma al’adunmu na gargajiya, ba ma wannan ba hatta addini bai amince da wasu daga cikinsu ba. Hakan ce ma ta saka a kullum mutuncinmu da kuma kwarjininmu suke zubewa a idanun duniya. Kuma wani abin takaici ma shi ne, irin wadannan tufafi da muke arowa ba su kai namu tafafin kwarjini da kima da mutunci ba. Domin wasu tufafin ma za ka ga bambancinsu da tsirara kadan ne ko ma a ce ba su da bambanci. Mallam Abubakar Ladan Yana cewa a wakar da ya rubuta:

“Kaya na sawa ba a fin mu daban-daban,

da Afirka, Esha, kasar Nasara gabadaya.

Hikimar mutan da ne da sunka yi kokari,

Mu ko kasala ta kashe mana zuciya”.