Friday, May 18, 2007

Hikimata

HARSHEN HAUSA DA KALUBALEN DA YAKE FUSKANTA.
A nan cikin Nijeriya harshen Hausa shi ne na daya a duk kasar, wajen yawan mutanen da suke amfani da shi. za a iya cewa harshen Hausa ya zama tafkin tsakiyar gari idan mutum bai sha ba to wani nasa ya sha. Ana iya cewa kusan ba lungu da sako da ba a magana da harshen Hausa a wannan nahiya.
Harshen Hausa mashahurin harshe ne a duniyar nan tamu,domin shahararsa ta kai ya goga ko ma ya yi kafada - da - kafada da dukkakn manyan harsunan duniya, domin harshe ne da yake da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su da bayyana kowanne irin tunani da su. Shi ya sa ma wani mawaki wato Malam Abubakar Ladan Zariya yake cewa a wakarsa:
"Harshenmu harshe ne a dangin harsuna,
Da muke gadara ko'ina nan duniya,

Har ma yi zaurance da waka ma da shi,
Tamkar su Turanci, Arab baki daya.

Za mu yi rubutu mu yi karatu ma da shi,
Mu alamta littaffai, jaridu bai daya.

Me zai hana ba za mu tashi mu girmama,
Harshe na kakanninmu babu kamar shiya."

Kamar yadda wannan mawaki ya fada, ana iya amfani da harshen Hausa wajen rubuta littattafai da jaridu da mujallu da kuma amfani da shi a kafafen yada labarai na radiyo da talabijin kai har ma da na'ura mai kwakwalwa.
Kodayake yaduwa da bunkasar harshen Hausa ba ya rasa nasaba da irin kwarjini da harshen yake da shi da kuma shaharar da Hausawa suka yi a fagen kasuwanci da fatauci. Hausawa sukan kutsa kowanne lungu da sako na wannan nahiya ta Afirka kai da ma duniya baki daya domin kai haja ko neman aiki ko neman ilmin addini da kuma yada shi. Haka kuma baki sukan yo takakka daga garuruwansu domin kawo haja da kuma saye a kasar Hausa. Wadannan da ma wasu dalilai suka sa harshen Hausa ya bunkasa ya shahara kuma ya gagara a wancan lokacin.
Kwarjini da kuma muhimmancin harshen Hausa a kullum kara bayyanuwa yake yi, kodayake har yanzu babu wata kasar Afirka ta yamma wadda ta mai da wannan harshe ya zama harshen kasa, amma a kan matsayinsa na farko daga cikin manyan harsunan Afirka, mutanen duniya suna daukan cewa babban kuskure ne idan aka banzatar da wannan harshe. Saboda haka manyan kasashen duniya kamar su: Amurka da Rasha da kasar Sin da Ingila da kuma Jamus suka ba wannan harshe babban muhimmanci. Kamar yadda kowa ya sani, wadannan manyan kasashe tuni suka fara yada labarai da harshen Hausa. Bayan haka wadannan kasashe suna kashe kudade da yawa wajen nazari da koyar da wannan harshe. Domin kuwa wani abin alfahari da tunkaho shi ne ba wata jami’a da ta yi shuhura a duniya da ba a koyar da harshen Hausa a cikinta. Wannan ma babban abin alfahari ne ga masu Magana da wanna harshe na Hausa. Kuma wani Karin abin alfahari ga wannan harshe da kuma masu Magana da shi, shi ne a jikin kudin kasarmu Nijeriya babu harshen wata kabila da aka yarda a yi amfani da shi sai harshen Hausa, ma’ana inda aka rubuta adadin kudin da Hausar ajami.
A nan gida Nijeriya haka zalika masana suna bayar da tasu gudummuwar ta fuskar himmatuwa wajen bincike da kuma bunkasa harshen, musamman ta fuskar rubuta littattafai da mukalu da wakoki, muna da irin wadannan mutane dubbai a cikin kasar nan kuma suna yin iya kokarinsu don ganin wannan harshe ya fadada kuma martabarsa ta karu a fadin duniya. Da akwai cibiyoyi da kungiyoyi da hukumomi wadanda suke karkashin wasu jami’o’i da kuma al’ummomin gari da suke ta yin aiki ba dare ba rana don ganin ci gaban wannan harshe.
Duk da irin wannan daukaka da kuma bunkasa da kuma kwarjini da wannan harshe yake da shi , wasu rukuni na mutane da ma daidaiku ba su ma san ana yi ba ‘wai kunu a wani gida’. Domin babban kalubalen da wannan harshen yake fuskanta shi ne, na rashin bin ka’idoji da dokoki da kuma tanade – tanaden wannan harshe. Wannan matsala tana ci wa manazarta da masana da kuma masu kishin wannan harshe tuwo a kwarya, domin matsalar ta zama ruwan dare, a inda za ka ga kafafen yada labarai musamman jaridu, wanda wasu da yawansu ba sa mutuntawa da kuma bin ka’idoji da kuma dokokin rubuta wannan harshe. Wannan babban kalubale ne da wannan harshe yake fuskanta, har ma wasu suna ganin cewa harshen Hausa ba shi da ma wasu tsayayyun ka’idoji da kuma dokoki. Har shi ne ma marigayi Dr. Akilu Aliyu yake cewa, a wakarsa ta “Bahaushe Mai Ban Haushi”

“Kwazo ya kyautu da mu nuna kuzari,
Inganta harshen namu shi ne Hausa.

Ku mu bar kasala sai mu himmatu kun ji,
Zazzage dantse nuna kishin Hausa.”

Haka ma marubuta littattafai, za ka ga wasu ko in ce da yawa daga cikinsu ba sa dora rubutunsu a mizanin wannan harshe, ma’ana ba sa bin dokoki da kuma ka’idojin wannan harshe. Don haka ne ma marigayi Dr. Akilu Aliyu ya kara da cewa:

“wannan abin kunya ina tamka tai,
Harshen wajen kakanka kai ka kasa,

Ya zam abin a yi dariya a yi gwalo,
A gareka don ka fadi ba shan fansa.”

Don haka ya zama wajibi a garemu da kuma duk wani mai sha’awar harshen Hausa, da mu himmatu wajen sani da kuma bin dokoki da kuma ka'idojin rubuta harshen Hausa.
Wata matsalar kuma da take ci wa wannan harshe tuwo a kwarya ita ce ta masu kafa allunan tallace - tallace na manya da kananan kamfanoni da ma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu, a inda za ka ga suna rubuta tallansu da kuma sanarwa da harshen Hausa yadda suka ga dama, ba tare da yin la'akari da dokoki da ka'idojin harshen ba. Wata Hausar ma da ake yin amfani ita a irin wadannan allunan talla , ba ma ta karantuwa.
Hanyoyin magance wadannan matsalaloli su ne:
Ya kamata kafafen yada labarai musamman ma na jarida su danga daukar kwararru, wadanda suka san ka'idoji da kuma dokokin wannan harshe na Hausa, domin kauce wa irin kurakuran da muka ambata a sama.
Bayan haka kuma manyan makarantu da jami'o'inmu musamman sashen koyar da harshen Hausa na wadannan makarantu, su tashi tsaye wajen fadakar da al'umma da kuma ilmantar da su, ta hanyar rubuce -rubuce da kuma bin diddigin irin wadannan kukrakurai domin kawo gyara.
Sannan kuma yana da kyau idan cibiyoyin nazarin Hausa a wadannan jami'o'i su dinga shirya bita akai -akai ga ma'aikatan yada labarai ('yan jarida) da kuma marubuta da masu buga takardu da littattafai domin ganin an kawar da wannan matsala baki daya.
Sai kuma shawara ta karshe, ya kamata su ma kansu malamai da suke koyar da harshen Hausa a makarantun Firamare da Sakandare, su dinga samin damar zuwa karop karatu akai - akai, idan ma haka ba ta samu ba, to, ya kamata a dinga shirya musu bita su ma daga lokaci zuwa lokaci.
Wadannan nan matakai idan aka bi su za a rage irin hawan kawarar da ake yi wa harshen Hausa. A karshe nake rufewa da wakar Malam Sa'adu zungur inda yake cewa:
"mu dai hakkinmu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.

Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da nadamar mai kin gaskiya."